Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Fa'iz Suraj yana fadar haka a yau talata bayan ganawarsa da Halifa Haftar babban komandan sojojin kasar Libya a birnin Paris na kasar Faransa, Suraj ya kara da cewa bangarorin biyu sun sami fahintar juna a kan tsagaita bude wuta da kuma zabe.
Ofishin shugaban kasar Faransa ma ta fitar da bayanin cewa, shuwagabannin kasar libyan guda biyu sun amince da aiwatar da yerjejeniyar Assukhairaat na kasar Morocc da kuma ci gaba da tattaunawa kan lamuran siyasar kasar.
Bayanin ya kara da cewa Suraja da Hfatar sun amince da cewa zasu yi kokarin ganin sun kafa tsarin democradia a kasar Libya, da kuma jujjuya iko a tsakanin yan siyasar kasar.
Kasar Libya dai ta cikin yake-yaken cikin gida tun bayan da kungiyar NATO ta taimakawa yan tawaye sun kifar da gwamnatin Kazzafi a shekara ta 2011.